Isa ga babban shafi
KENYA - Wasanni

An kama wanda ya kashe matar sa 'yar tseren Kenya

Jami’an tsaron Kenya sun damke Ibrahim Rotich, mijin shaharerriyar ‘yar tseren kasar ta Kenya Agnes Tirop, kan kisan da ake zargi ya yi wa mai dakin na sa ta hanyar daba mata wuka, a wani lamari da ya girgiza kasar ta Kenya da duniyar wasannin guje-guje.

'Yar tseren Kenya Agnes Tirop a watan Mayun shekarar 2018 a Doha, na kasar Qatar
'Yar tseren Kenya Agnes Tirop a watan Mayun shekarar 2018 a Doha, na kasar Qatar KARIM JAAFAR AFP/Archives
Talla

Sashin binciken manyan laifuka na kasar ya bayyana cewa an kama Rotich ne da yammacin ranar Alhamis a gundumar Mombasa a daidai lokacin da yake kokarin tsrewa daga kasar.

Rotich ya kasance babban wanda ake zargi kan kisan gillar, ‘yar tseren mai shekaru 25 da ta lashe kambin zinare a gasar zakarun duniya da kuma na Olympic.

A ranar Alhamis ne hukumomin Kenya suka sanar da mutuwar Agnes Tirop wanda ke rike da kambin gudun mita dubu 5 na duniya a gidanta, kuma nan take hukumomi suka daura alhakin kissan ga mijin nata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.