Isa ga babban shafi
Wasanni

Tokyo Olympics: Dan kasar Kenya ya lashe lambar zinare a tseren mita 800

Dan wasan tseren gudu na kasar Kenya Emmanuel Korir ya lashe tseren mita 800 na maza a gasar wasannin Olympics da ke gudana a birnin Tokyo na kasar Japan a yau Laraba, haka kuma abokinsa dan Kenyan Ferguson Rotch ya lashe lambar azurfa.

Dan wasan tsere na Kenya, Emmanuel Korir.
Dan wasan tsere na Kenya, Emmanuel Korir. Reuters
Talla

Korir ya  kammala gudun ne a cikin dakikoki 45 da digo 6, inda shi Rocht ya lashe lambar azurfa ta wajen kammalawa a cikin minti 1 dakikoki 45 da digo 23, yayin da shi kuma wanda ya lashe tagulla, Patryk Dobek ya kammala a cikin minti 1 da dakikoki 45 da digo 39.

Koriri ya gaji dan kasar Kenyan nan ne David Rudisha, wanda ya gaza zuwa kare kambinsa sakamakon rauni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.