Isa ga babban shafi
Wasanni-Tennis

Olympics a Tokyo: Lamba 42 a duniya ta yi waje da Naomi Osaka

An yi waje da shahararriyar ‘yar wasan kwallon Tennis, ‘yar kasar Japan Naomi Osaka a gasar wasanni ta Olympics da ke gudana a halin yanzu a birnin Tokyo na Japan.

Naomi Osaka in action during her defeat to Marketa Vondrousova at the Tokyo Olympics
Naomi Osaka in action during her defeat to Marketa Vondrousova at the Tokyo Olympics Tiziana FABI AFP
Talla

Osaka ta sha kashi ne a gida a hannun ‘yar wasan Tennis ta kasar Czech Marketa Vondrousova.

Osaka mai shekaru 23 tana cikin ‘yan wasan da suka tallata wannan gasa ta babban birnin kasar Japan, har ma ta samu karramawar kunna wutar gasar a bikin bude ta a makon da ya gabata.

 Amma sai ga shi ‘yar wasan Tennis din da sau 4 tana lashe babban kofin Tennis na Grand Slam ta gaza tabuka wani abu, inda ta yi rashin nasara  6-1  6-4 a hannun ‘yar wasan da ke lamba 42 a duniya a harkar Tennis a cikin zagaye na 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.