Isa ga babban shafi
Wasanni

Gasar neman cin kofin Us Open na Tennis

Bayan gaggarumar nasara da ya samu kwanaki biyu da suka gabata a gasar Us Open na Tennis a yayin fafatawa tsakanin Andy Murray da Yoshinto Nishioka, dan kasar Birtaniya Andy Murray ya kasa tsallakawa mataki na gaba a yayin da ya fafatawa da dan kasar Canada Felix Auger Aliassime.

Gasar cin kofin Tennis na Us Open
Gasar cin kofin Tennis na Us Open cc0 Pixabay/HeungSoon
Talla

Dan kasar Canada Felix Auger Aliassime ya samu nasara a kan dan wasan Birtanaya Andy Murray da ci 6 da 2.6 da 3. Sai 6 da 4 a daren jiya lokacin da suka fafata a New York a gasar ta Us Open.

Matteo Berrettini dan kasar Italiya ya lalllasa Ugo Hembert Bafaranshe da ci 6 da 4,6 da 4 kana 7 da 6.

Casper Ruud dan kasar Norway ya tsallaka mataki na gaba bayan da ya doke Emil Ruusuvuori dan kasar Finland da ci 6 da 4. 6 da 3 kana 3 da 2.

Alex de Minaur dan kasar Austria ya doke Richard Gasquet ban asalin kasar Faransa da ci6 da 4,6 da 3 sai 7 da 6.

Bangaren mata

Madison Keys yar kasar Amurka ta doke Aliona Bolsova yar Spain da ci 6da 2.6 da 1.

Alize Cornet daga Faransa ta lallasa Ysaline Bonaventure daga Belgium da ci 7 da 6, 7 da 4 sai 6 da 3.

Donna Vekic daga Crotia ta doke Patricia Tig daga Roumania da ci 6 da 2 sai 6 da 1.

Serena Williams daga Amurka ta doke Marganita Gasparyan da ci 6 da 2,sai 6 da 4.

Ons Jabeur daga Tunisia ta doke Kala Kanepi daga Estonia da ci 7 da 6,6 da nema.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.