Isa ga babban shafi
Wasanni

Damuwa ta hana Osaka buga gasar French Open

Magoya baya a Japan da wasu fitattun mutane sun fito sun nuna goyon baya ga tauraruwar kwallon Tennis lamba ta biyu a duniya, wato Naomi Osaka tare da tausaya mata bayan ta janye daga gasar French Open saboda damuwa

Naomi Osaka
Naomi Osaka Paul CROCK AFP/File
Talla

‘Yar wasan ta bayyana cewa, tana fama da larurrar damuwa na tsawon lokaci, abin da ya hana ta halartar taron manema labarai a gasar ta French Open.

Sai dai bisa dukkan alamu mahukuntan gasar ba su ji dadin yadda Osaka ta kaurace wa taron manema labaran ba, inda har suka yi barazanar korar ta daga gasar.

Bayan wannan barazanar ce, ‘yar wasan ta fitar da wata sanarwa da ke cewa, ta janye daga gasar, kuma za ta yi nisa da filin kwallon Tennis na wani lokaci.

Yanzu haka magoya bayanta sun mara mata baya, suna shawartar ta da ta dauki dogon lokaci na hutu, inda ma wasu ke cewa, bai kamata ta wakilci Japan a gasar Olympics ta Tokyo  tsakanin watan Yuili zuwa Agusta.

Osaka na daya daga cikin fitattun ‘yan wasan da ake sa ran za su halarci gasar Olympics a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.