Isa ga babban shafi
Tennis - Tokyo

Fitattun 'yan wasan Tennis sun janye daga shiga gasar Olympics

Angelique Kerber ta zama fitacciyar yar kwallon Tennis da ta janye daga shiga gasar Olympics da ake gaf da farawa a birnin Tokyo na kasar Japan.

Angelique Kerber fitacciyar 'yar wasan Tennis ta kasar Jamus
Angelique Kerber fitacciyar 'yar wasan Tennis ta kasar Jamus Adrian DENNIS AFP/Archives
Talla

Cikin sanarwar da ta fitar Kerber mai shekaru 22 yar kasar Jamus, ta bayyana gasar ta Olympics a matsayin babban burinta, musamman a cikin watannin baya bayan nan.

Yayin gasar Olympics ta karshe da ta gudana a birnin Rio na Brazil, lambar Azurfa bajamushiyar mai shekaru 33 ta lashe a wasan Tennis, yayin da kuma a shekarar 2012 Kerber ta gaza tsallake zagayen kwata finals a wasan Tennis din da ya gudana a gasar Olympics da birnin London ya karbi bakunci.

Zuwa yanzu fitattun yan wasan Tennis da suka janye daga shiga gasar Olympics ta birnin Tokyo sun hada da Roger Federer, Rafael Nadal, Serena Williams da kuma Dominic Thiem, a yayin da zakaran bana na gasar Wimbledon wato Novak Djokovic ya ce har yanzu bai yanke shawarar shiga gasar Olympics din ta bana ba ko kuma a a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.