Isa ga babban shafi
Wasanni - Tennis

Djokovic ya lashe manyan kofunan gasar Tennis 3 cikin shekara 1

Novak Djokovic dan kasar Serbia ya lashe kofin gasar Wimbledon ta bana bayan samun nasara kan abokin karawarsa Matteo Berrettini na kasar Italiya da kwallaye 6-4, 6-4, 6-3.

Fitaccen dan wasan kwallon Tennis lamba a duniya Novak Djokovic, bayan lashe kofin gasar Wimbledon.
Fitaccen dan wasan kwallon Tennis lamba a duniya Novak Djokovic, bayan lashe kofin gasar Wimbledon. Adrian DENNIS AFP
Talla

Karo na 6 kenan da Djokovic ke lashe kofin gasar Wimbledon, a yayinda kuma ya lashe jumillar kofunan gasar Grand Slam 20, bayan lashe kofunan wasannin French Open da Australian Open da suka gudana a bana.

Nasarorin da Djokovic ya samu ya bashi samar kafa tarihin zama dan wasan tennis na biyar a duniya da ya lashe manyan kofunan gasar Grand Slam uku a kakar wasa guda, tun bayan Rod Lover na kasar Australia a shekarar 1969.

Wani tarihin kuma da Novak Djokovic ya kafa shi ne na shafe kwanaki 329 a matsayin fitaccen dan wasan kwallon Tennis lamba daya a duniya da maki dubu 12 da 113, kamar yadda hukumar wasannin Tennis ta duniya ta bayyana a jiya Litinin.

Danilil Medvedev na Rasha ke biye a matsayi na biyu da maki dubu 10 da 370, yayin da Rafeal Nadal na Spain ke matsayi 3 wajen kwarewa a duniya da maki dubu 8 da 270.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.