Isa ga babban shafi
Wasanni

Bukatar samar da daidaiton albashi tsakanin 'yan wasa Maza da Mata

Wani Bincike ya nuna yadda akasarin wasanni ke biyan Yan wasa albahsi kusan daya tsakanin maza da mata, sabanin yadda ake samun wagigin gibi a bangaren kwallon kafa.

Tsohowar 'yar wasan Kriket ta kasar New Zealand a bangaren mata, an dauki hoton a watan Oktoban 2018
Tsohowar 'yar wasan Kriket ta kasar New Zealand a bangaren mata, an dauki hoton a watan Oktoban 2018 AFP/File
Talla

Wasannin kurket yayi nasarar shawo kan wannan matasala wajen baiwa Yan wasa maza ad mata da suka samu nasara makudan kudade ba tare da nuna fifiko tsakanin jinsi ba.

Haka wasannin kwallon sanda da kwallon bango suma basa banbanta bioyan maza da mata, yayin da a bangaren wasan tennis ma an dade ana fuskantar haka.

Mataimakiyar kaftin din kungiyar kwallon kurket na Ingila, Anya Shrubsole tace "wannan wani yakin hadin kai ne domin rage banbancin da ake nunawa ‘yan wasa mata da maza."

Kaftin din kwallon sandan Ingila Hollie Pearne-Webb ya bukaci masu jagorancin kwallon kafa da su duba irin cigaban da suka samu domin kwaikwayo.

Toh ko menene bangaren kwallon kafa zai koya wajen daidaita kudaden da ake baiwa maza da mata?

Wannan itace mahawarar da ake cigaba da yi tsakanin 'Yan wasa da masu jagorancin wasan da kuma masu fafutukar ganin an samu daidaito tsakanin jinsina.

Shrubsole tace "har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da bukatar biyan ‘yan wasa kudi guda tsakanin maza da mata."

Jami’ar tace a wasannin bazarar bana, kowacce kungiya zata samu kyautar Dala 150,000 idan ta samu nasara, amma kuma albashin ‘yan wasan ya banbanta, inda ake biyan maza tsakanin Fam 24,000 zuwa 100,000, yayin da su kuwa mata za’a niya su tsakanin Fam 3,600 zuwa 15,000.

Sai dai Shrubsole tace wannan nada nasaba da yawan `Yan kallon dake halartar filayen wasanni suna biyan kudi, inda ake samun mutane da yawa a wasannin maza sabanin na mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.