Isa ga babban shafi
Tokyo 2020

An kaddamar da gasar Olympics ta Tokyo 2020

An kaddamar da gasar wasanni  ta Olympics a wannan Juma’a a filin wasa da kusan babu kowa a cikinsa, bayan da aka jinkirta gasar tsawon shekara guda  sakamakon bullar annobar Covid-19.

Wutar da aka kunna domin kaddamar da gasar Tokyo 2020
Wutar da aka kunna domin kaddamar da gasar Tokyo 2020 REUTERS - MARKO DJURICA
Talla

An fara bikin ne  da nuna wani  hoton bidiyo na ‘yan wasan motsa jiki suna atisaye a gida  a lokacin dokar kullen da kasashe suka sanya, sakamakon bullar annobar Coronavirus, sai kuma aka saki tirtsitsin wuta da ya lula can cikin samaniya.

An gudanar da wannan biki  ne a gaban ‘yan daruruwan jami’ai  da manyan baki da suka hada da Sarkin Japan, Naruhito da shugaban Faransa Emmanuel Macron da kuma uwargidar shugaban Amurka Jill Biden, duk da cewa filin wasan da ake bikin zai iya daukar ‘yan kallo dubu 68.

Shahararriyar ‘yar wasan kwallon Tennis ‘yar asalin Japan, wato Naomi Osaka ce ta kunna wutar kaddamar da wasannin na Olypmics na Tokyo 2020.

Gasar ta Olympics ta fuskanci adawa mai tsanani a Japan, sakamakon fargabar cewa tarin ‘yan wasan motsa jiki har dubu 11 ka iya ta’azzara yaduwar annobar Covid-19.

Masu shirya gasar sun sanya matakan kariya masu tsauri, inda suka haramta wa ‘yan kallo daga kasashen waje zuwa kashe kwarkwatar idanu a  karon farko, kana suka takaita filayen wasannin da ‘yan kallo na cikin gida za su iya shiga.

Birnin Tokyo da ke karbar bakuncin gasar na fuskantar ta’azzarar annobar Korona, kuma yana karkashin dokar ta baci, inda dole aka rufe mashaya da gidajen cin abinci daga karfe 8 na dare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.