Isa ga babban shafi

Kenya za ta yi wa marigayi Kibaki jana'iza ta ban girma

Gwamnatin kasar Kenya za ta gudanar da jana'izar girmamawa ga tsohon shugaban kasar Mwai Kibaki, wanda ya jagoranci kasar da ke gabashin Afirka tsawon fiye da shekaru goma.

Tsohon shugaban kasar Kenya marigayi Mwai Kibaki.
Tsohon shugaban kasar Kenya marigayi Mwai Kibaki. AFP/Tony KARUMBA
Talla

Kibaki wanda ya rasu yana da shekaru 90 a duniya, ya zama shugaban kasar Kenya na uku daga watan Disamban shekarar 2002 zuwa Afrilun 2013, inda ya karbi ragamar mulkin kasar daga mulkin kama karya na Daniel arap Moi.

Ministan harkokin cikin gidan Kenya Fred Matiangi ya ce za a binne marigayi Kibaki a ranar Asabar mai zuwa a gidansa da ke Othaya a tsaunin Nyeri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.