Shugaba Kenyatta ya bayyana damuwa akan halin da talakawan kasar suka shiga
Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana damuwa akan halin da talakawan kasar suka shiga na tsadar rayuwa, musamman hauhawan farashin kayan abinci, cikin su harda masara.
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar ta Kenya Uhuru Kenyatta ya bukaci daukacin yan kasar da su bayar da goyon bayan da ya dace ga Gwamnatin kasar duk da cewa da sauran aiki a gaban wannan gwamnati.
Shugaban ya na mai cewa wannan dace ne akayi cewar yan kasar na fuskantar karancin abinci kafin lokacin da ake gudanar da kowane zabe? Wannan sakamakon yadda harakokin kasuwanci ke gudana ne, ko kuma wani shiri ne na musamman?
Sanya siyasa cikin halin rayuwar talakawa na kasar Kenya, ba tare da samar da maslaha ba, wani yunkuri ne na shagube ga mutanen da kuke bukata su zabe ku. Kulla dangantaka tsakanin jama’a da yan siyasa ya zama wajibi domin tallafawa jama’ar kasar mu. Amma idan hakan ya haifar da matsaloli kamar tsadar masara duk lokacin gudanar da zabe, hakki ne akan mai zabe ya kawo karshen haka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu