Isa ga babban shafi

Kenya ta musanta zargin kin biyan China kudin ruwa a bashin ginin layin dogo

Kenya ta musanta cewa ta ki biyan kudin ruwa kan rancen da kasar China ta bata, na gina titin jirgin kasa daga birnin Mombasa mai tashar jiragen ruwa zuwa wasu sassan kasar, layin dogon da ya fara aiki a shekarar 2017.

Shugaba William Ruto na Kenya.
Shugaba William Ruto na Kenya. REUTERS - MONICAH MWANGI
Talla

Aikin da ya lakume dalar Amurka biliyan 5, wanda kasar Sin ta dauki nauyin kashi 90 cikin 100 na sa, ya maye gurbin titin jirgin kasan da ake kira da "Lunatic Express", wanda kasar Birtaniya ta ginawa Kenya a zamanin mulkin mallaka, fiye da karni daya da ya gabata.

Jaridar Business Daily ta kasar Kenya ta rawaito cewa, gwamnatin kasar ta gaza biyan kudin ruwa a cikin shekarar da ta kare a watan Yuni, lamarin da ya sanya dole gwamnatin Kenyan ta biya tarar kudin kasar na shilling biliyan 1.312, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 10.8.

Sai dai sakataren baitul malin kasar Ukur Yatani ya yi watsi da rahoton, wanda ya ce babu gaskiya a cikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.