Isa ga babban shafi

Kenya za ta koma sayen man fetur daga Rasha

Shugaba William Ruto na Kenya ya bayyana aniyar kasar kan fara sayen man fetur daga Rasha a sassauta tsadar rayuwar da kasar ke gani wadda ake alankatawa da tashin farashin man.

Shugaba William Ruto na Kenya.
Shugaba William Ruto na Kenya. REUTERS - MONICAH MWANGI
Talla

Matakin na shugaba Ruto na zuwa ne a dai dai lokacin da manyan kasashen Duniya musamman Amurka ke kauracewa cinikayya da Rasha saboda mamayar da ta ke yi wa Ukraine.

A zantawarsa, shugaba William Ruto ya ce zai yi amfani da kowacce dama da ta zo mishi wajen rage radadin rayuwar da al’ummar Kenya ke fama da ita.

Ruto ya bayyana cewa karancin man fetur ne ya haddasa tsadarsa a kasar wanda ke da nasaba da wahalar da al’ummar Kenya ke fama da ita a yanzu, dalilin da ya dole ya yi dukkanin mai yiwuwa wajen warware matsalar.

Shugaban ya ce Kenya za ta nemi fetur daga dukkanin kasar da za ta iya wadata ta da makamashin ba tare da la’akari da ko wacce ce ba, domin abu mafi muhimmanci shi ne saukakawa al’ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.