Isa ga babban shafi

Sabon shugaban Kenya ya fara aiki gadan-gadan

Sabon shugaban Kenya William Ruto ya sanar da sabbin tsare-tsarensa na bunkasa tattalin arzikin kasar, yayin da ya yi wa al’ummarsa alkawarin mutunta su baki daya.

Shugaban Kenya William Ruto
Shugaban Kenya William Ruto REUTERS - BAZ RATNER
Talla

Jim kadan da karbar rantsuwar kama-aiki a gaban dubban jama’ar Kenya da suka hallara a filin wasan na birnin Nairobi mai yawan kuejru dubu 60, sabon shugaban ya nada alkalai 6 da a can baya tsohon shugaban kasar Uhuru Kenyatta ya ki amincewa da su.

Kazalika Mista Ruto ya rubanya kason da ake ware wa bangaren shari’ar kasar zuwa biliyan uku a kasafin kudi na shekara.

Har ila yau shugaba Ruto ya ce, tabbas zai rikito da farashin taki zuwa Shilling dubu 3 da 500 daga Shilling dubu 6 da 500.

Sabon shugaban zai kuma  kawar da kudin rarar man fetur da masara, yayin da kuma zai kafa wani asusun tallafa wa matasa masu zafin neman na kansu wadanda kuma ke kananan sana’o’i.

Shugaba Ruto ya kuma dauki matakin bude tashar jiragen ruwa ta Mombasa, sannan  ya ce, za su sake nazartar tsarin nan na sanya ido kan hada-hadar kudaden da yawansu ya zarta Shilling miliyan guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.