Isa ga babban shafi

Sauyin yanayi: Masu zanga-zangar a Kenya sun nemi kasashen yamma su biya Afirka diyya

Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a titunan birnin Nairobi don neman kasashe masu karfin tattalin arziki da su kara kaimi wajen magance sauyin yanayi a Afirka.

Masu zanga-zangar na zargin manyan kasashe da jefa nahiyar Afirka cikin mummunan yanayin da ta tsinci kanta
Masu zanga-zangar na zargin manyan kasashe da jefa nahiyar Afirka cikin mummunan yanayin da ta tsinci kanta REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Yankunan kasar Kenya sun fuskanci bala'in fari mafi muni tun bayan shekaru arba'in wanda da dama ake dangantawa da dumamar yanayi.

Abin da ya sanya masu fafutuka ke cewa ya kamata kasashe masu arzikin masana'antu su biya su diyya kan asarar da suka yi.

Masu zanga-zangar dai sun gudanar da tattakin ne a matsayin wani bangare na nuna adalci ga nahiyar Afirka wajen yaki da dumamar yanayi.

Kungiyoyin masu fafutuka dai na neman kasashe masu arziki su biya diyyar barnar da aka yi wa kananan manoma da makiyaya a fadin Afirka.

A watan Satumban 2021 kusan 'yan Kenya miliyan 3.5 ne suka shiga cikin yanayin kunsi sakamakon sauyi yanayi, inda gwamnati ta ayyana shi a matsayin bala'i mafi muni a kasar.

A lokaci guda kuma, mutane kusan 200,000 ne suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.