Isa ga babban shafi

Manoma a Kenya sun bukaci gwamnati ta janye kudirin noma wani sabon iri na hatsi

Kungiyoyin fararen hula da na manoma sun bukaci gwamnatinm kasar Kenya da ta sake matsayin ta dangane da cire dokar haramta amfani da hatsin da irin da aka sauyawa kwayar halitta, yayin da kasar ke fama da matsalar fari.

Yadda ake horas da yara harkar noma a gabashin Kenya.
Yadda ake horas da yara harkar noma a gabashin Kenya. © RFI/Victor Moturi
Talla

Wannan bukata ta biyo bayan matakin da sabuwar gwamnatin kasar ta shugaba William Ruto ta dauka a ranar litinin, na bada damar noma irin wannan iri da aka sauyawa kwayar halitta, domin shawo kan matsanancin farin da ya addabi kasar, wanda shine irinsa mafi muni a cikin shekaru 40.

Sai dai kungiyoyin sun bayyana damuwa akan sahihancin irin wadannan hatsi a sanarwar hadin gwiwar da suka rabawa manema labarai wanda ya hada da kungiyar ‘Greenpeace ta Afirka‘.

Sanarwar tace samar da abinci ga jama’a ya zama wajibi yayi dubi akan ingancin sa da kuma lafiyarsa, yayin da ake fargabar irin hadarin da wannan nau’i ke da shi saboda yadda ake amfani da sinadarai masu hadari ga jama’a.

Kasar Kenya kamar wasu kasashen Afirka da dama sun haramta amfani da nau’in abincin da aka sauyawa kwayar halitta saboda kare lafiyar jama’ar su.

Sai dai fadar shugaban kasar William Ruto ta bayyana halarta irin wannan abincin a matsayin ci gaba domin samar da irin da kwari basa iya lalatawa.

Kenya na daya daga cikin kasashen Afrika ta Gabas dake fama da tsananin fari wanda ya yi yiwa aikin noma da kiwo illa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.