Isa ga babban shafi

Ana ci gaba da kashe fararen hula a yankin Tigray. -Gebreyesus

Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Gebreyesus yayi zargin cewar sojojin kasashen Eritrea da Habasha na ci gaba da kai munanan hare hare a yankin Tigray inda suke kashe fararen hula ba tare da kaukautawa ba.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus. © AP - Salvatore Di Nolfi
Talla

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gebreyesus yace ana iya ceto rayukan fararen hular da ake kaiwa hari amma hakan bai yiwu ba saboda yadda hare haren ke gudana.

Shugaban Hukumar ya bukaci kawo karshen kawanyar da aka yiwa yankin domin ceto rayukan jama’a.

Gwamnatin Habasha da mayakan Tigray sun bayyana shirin shiga tattaunawar zaman lafiya da kungiyar kasashen Afirka ke jagranci, amma har ya zuwa wannan lokaci ana ci gaba da fafatawa tsakanin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.