Isa ga babban shafi

Jami'an tsaro sun kashe fararen hula da dama a Habasha - Bincike

Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Habasha ta ce jami’an tsaro sun kashe fararen hula da dama a Gambella a watan Yuni, bayan zargin su da hada baki da ‘yan tawaye, abin da ya haifar da wani hari a Kudu maso yammacin kasar.

Wani dakin ajiye gawarwaki da aka fi sani da mortuary a turance. (An yi amfani da wannan hoto domin misali kawai)
Wani dakin ajiye gawarwaki da aka fi sani da mortuary a turance. (An yi amfani da wannan hoto domin misali kawai) AFP
Talla

Hare-haren na hadin guiwa a ranar 14 ga watan Yuni da kungiyar ‘yan tawayen Gambella da kungiyar ‘yan tawayen Oromo, da gwamnatin Habasha ta yi wa lakabi da kungiyar ta’addanci, ya haifar da harbe-harbe na tsawon sa’o’i.

Bayan da sojoji suka yi nasarar dakile harin, dakarun yankin sun kashe duk wanda ake zargi da hannu ko kuma hada baki a harin.

A baya dai kungiyar kare hakkin mai zaman kanta ta zargi jami’an tsaro da aiwatar da hukuncin kisa yayin da suke shiga gida-gida, a cewar wata sanarwa da ta fitar kwanaki bayan harin.

Wadanda lamarin ya rutsa da su sun hada da masu tabin hankali, yayin da wasu akalla 25 suka samu raunuka, tare da azabtar da wasu daga cikin mazauna garin.

Hukumar kare hakkin bil adama ta ce mayakan sun kashe farar hula bakwai, yayin da wasu mutane shida suka mutu lokacin da ake musayar wuta tsakanin ‘yan tawaye da sojoji.

Rundunar ‘yan sandan yankin ta ce ‘yan tawaye ne suka kashe fararen hula, kuma babu wanda ya yi ikirarin gawarwakin da hukumomin yankin suka binne.

Yankin Gambella dai ya yi iyaka da Sudan ta Kudu kuma a baya ya sha fama da tashin hankali daga mayakan da ke makwabtaka da kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.