Isa ga babban shafi

Habasha: 'Yan tawayen Tigray sun janye daga yankin Amhara zuwa arewacin kasar

Mahukuntan 'yan tawayen Tigray sun ce sun janye sojojinsu daga yankunan da suka mamaye a yankin Amhara, domin fuskantar farmakin hadin gwiwa da sojojin Habasha da na Eritriya suka yi a arewacin kasar.

Mayakan sun ce sun shirya tunkarar dakarun hadin gwiwa na gwamnatin kasar da kuma na Eritrea
Mayakan sun ce sun shirya tunkarar dakarun hadin gwiwa na gwamnatin kasar da kuma na Eritrea AFP - EDUARDO SOTERAS
Talla

Bayan tsagaita bude wuta na tsawon watanni biyar, an sake gwabza fada a karshen watan Agusta tsakanin gwamnatin Habasha da ke samun goyon bayan sojoji da mayakan sa kai na yankin Amhara da kuma 'yan tawayen Tigray.

Gwamnatin Asmara, wacce ke adawa da shugabannin 'yan tawayen Tigrai, ita ma tana taimakawa sojojin Habasha, kamar yadda ta yi a lokacin farkon rikicin da ya fara a watan Nuwamban 2020, inda aka tuhumi sojojin Eritrea da laifuka da dama.

"An sauyawa dakarun mu alkibla ne don tunkarar sojojin hadin gwiwa da suka mamaye kudancin kasar, saboda haka mun yi kaura daga yankin Amhara da muka shiga," in ji babban kwamandan 'yan tawaye a Tigray a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce, an aiwatar da shawarar ne a cikin kwanaki uku da suka gabata, inda ta ba da tabbacin cewa, "duk da cewa makiya sun yi kokarin shammata, amma ba su yi nasarar sauya lamarin ba, sai dai ya kara tsananta wa.

Yankunan da ake gwabza fada an hanawa ‘yan jarida damar zuwa, kuma har yanzu babu wani karin bayani wajen tabbatar da ikirarin ‘yan tawayen na Tigray.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.