Isa ga babban shafi

Mun shirya shiga tattaunawar zaman lafiya da Habasha a karkashin AU - TPLF

'Yan tawayen Tigray na kasar Habasha sun ce a shirye suke su shiga tattaunawar zaman lafiya tsakaninsu gwamnati, wadda kungiyar Tarayyar Afirka AU za ta jagoranta, domin kawo karshen fadan da aka shafe kusan shekaru biyu ana gwabzawa.

Wasu mayakan sa kai daga yankin Amhara don tunkarar kungiyar TPLF a ranar 9 ga Nuwamba, 2020.
Wasu mayakan sa kai daga yankin Amhara don tunkarar kungiyar TPLF a ranar 9 ga Nuwamba, 2020. REUTERS/Tiksa Negeri//File Photo
Talla

Sanarwar da ‘yan tawayen na Tigray suka fitar ta zo ne a daidai lokacin da hukumomin kasa da kasa ke kokarin warware kaamin rikicin da ya tagayyara miliyoyin mutane a yankin dake arewacin kasar Habasha.

Kawo yanzu dai babu wani karin haske daga gwamnatin kasar Habasha, wadda ta dade tana nanata cewa duk wani shirin samar da zaman lafiya dole ne kungiyar AU mai hedikwata a Addis Ababa ta shiga tsakani.

Sai dai har ya zuwa yanzu kungiyar ‘yan tawayen Tigray TPLF na cigaba da yin suka kakkausa ga matsayin wakilin da kungiyar AU ta turo musu Olusegun Obasanjo, wanda suka ce basu aminta da shi ba, saboda kusancinsa da Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.