Isa ga babban shafi

'Yan tawayen Tigray sun musanta ikirarin MDD kan satar fetur din WFP

Jagororin ‘yan tawayen yankin Tigray da ke arewacin kasar Habasha sun musanta zargin da majalisar dinkin duniya  ta yi musu na satar man fetur daga rumbunan ajiyar kayayyakin hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP.

'Yan tawayen Tigray na Habasha.
'Yan tawayen Tigray na Habasha. AP - Ben Curtis
Talla

Shugaban hukumar ta WFP David Beasely ya ce mayakan na Tigray sun kuntuka satar ce a ranar Larabar da ta gabata, ranar da sabon fada ya barke tsakanin ‘yan tawayen da sojojin gwamnati, lamarin da ya wargaza yarjejeniyar tsagaita wutar da bangarorin biyu suka cimma a cikin watan Maris.

Sai dai gwamnatin yankin na Tigray ta bayyana zargin a matsayin maras tushe, domin a cewar ta ta kwashe litar man fetur 600,000 da ta bai wa hukumar samar da abincin ta majalisar dinkin duniya a matsayin aro a watannin baya.

Rashin zaman lafiya ya dawo a yankin Tigray bayan da bangarorin da ke rikici da juna suka dawo da farmakin da su ke kaiwa a farkon makon nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.