Isa ga babban shafi

Habasha ta amince da fara tattaunawa da 'yan tawayen Tigray- AU

Kungiyar Tarayyar Afrika ta ce gwamnatin Habasha ta bata tabbacin amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin dakarunta da ‘yan tawayen yankin Tigray, karon farko da mahukuntan kasar ke tabbatar da jita-jitar yiwuwar dawowar yakin tsakanin bangarorin biyu.

Firaministan Habasha Abiy Ahmed.
Firaministan Habasha Abiy Ahmed. AFP - AMANUEL SILESHI
Talla

Tsawon lokaci gwamnatin ta Habasha ta shafe ta na yaki da ‘yan tawayen na Tigray, sai dai a makwannin baya baya nan dukkanin bangarorin biyu sun amince da shirin kawo karshen yakin watanni 21 inda gwamnatin kasar ta bukaci AU ta shiga tsakani.

A bangare guda ‘yan tawayen na Tigray sun bukaci shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya shiga tsakani don kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu da gwamnatin ta Habasha.

Jakadan Kungiyar AU tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yanzu haka na jagorantar kokarin kawo karshen rikicin na Habasha ta fuskar Diflomasiyya.

Cikin wata sanarwa da AU ta wallafa ta tabatar da yadda a karon farko aka yi tattaunawa tsakanin firaminista Abiy Ahmed da jagoran ‘yan tawayen na Tigray Debretsion Gebremichael wanda ya bukaci sake gina yankin gabanin shiga tattaunawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.