Isa ga babban shafi

Al-Shabaab ta kai hari wani sansanin soji da ke kan iyakar Somaliya da Habasha

Mayakan Al-Shabaab sun kai hari kan wani sansanin soji da ke kan iyakar Somalia da Habasha a ranar Juma'a, inda suka yi kazamin fada da ya yi sanadin rasa rayuka da ba a san adadinsu ba.

Mayakan Al-Shabaab na kasar Somalia
Mayakan Al-Shabaab na kasar Somalia RFI-Swahili
Talla

 

Wata Majiyar ta ce, an kai harin ne a sansanin da ke Ato, inda aka yi artabu da sojojin Habasha da kuma wadanda ake kira ‘yan sanda na musamman na Liyu daga yankin Somaliya na kasar.

Sai dai kuma kamfanin dillancin labaran kasar Habasha ya nakalto Manjo Janar Tesfaye Ayalew na rundunar tsaron kasar yana cewa kungiyar al-Shabaab ta yi kokarin kutsawa daga kan iyakar kasar amma aka dakile ta kuma ta yi asara mai yawa.

Alhakin harin

Kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin a cikin wata ‘yar gajeruwar sanarwa, inda ta ce mayakanta sun mamaye sansanin tare da kashe ‘yan sandan Habasha sama da 100.

Kawo yanzu dai babu wani martani kan bukatar da kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar na neman karin haske daga mahukuntan yankin Somaliya na kasar Habasha.

Wannan dai shi ne hari na baya bayan nan da mayakan masu ikirarin jihadi da ke Somaliya suka kai Habasha cikin kasa da makwanni biyu, lamarin da ya haifar da fargaba game da zaman lafiyar kan iyaka da kuma wata sabuwar dabara ta kungiyar mai alaka da Al-Qaeda ke amfani da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.