Isa ga babban shafi

Mayakan Al Shebab sun kai hari sansanin Sojan Somalia

Mayakan Al-Shebaab sun kai farmaki kan wani sansanin sojojin Somalia, inda kuma suka sake karbe iko da wani gari da dakarun gwamnatin kasar suka kwace daga hannunsu a farkon wannan watan da muke ciki.

Wasu daga cikin mayakan kungiyar Al Shebab
Wasu daga cikin mayakan kungiyar Al Shebab AFP/TOPSHOTS/STRINGER
Talla

Mazauna yankin sun ce, da sanyin safiyar yau Talata, mayakan suka fara kaddamar da harin kunar bakin wake da nufin halaka sojojin gwamnati.

Mayakan Al Shebab
Mayakan Al Shebab (Photo : Reuters)

Kodayake rahotanni sun ce, tuni sojojin suka mayar da martani ta hanyar yi wa mayakan luguden wuta ta sama.

Ko a cikin watan Afrilu, Al Shabab ta bayyana cewa ta kai hare-hare rabin dozin, ta ce ta kashe sojojin kungiyar tarayyar Afrika 59 mafiya yawansu kuma sojojin kasar Uganda ne, a yayin da su kuma suka ce an kashe masu rasa mayaka 14.

Daga nasu bangaren Dakarun Uganda sun bayyana mutuwar sojojinsu 4 ne, ba kamar yadda al Shebab ta sanar ba, a yayin da su ka ce sun kashe mayakan na Shebab 22.

Mafi yawan hare haren dai, an kai su ne ta hanyar harba rokoki kan sansanonin sojin samar da zaman lafiyar na Amisom dake da sansani a yankin na Bas-Shabelle.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.