Isa ga babban shafi
Somalia-Farmajo

Shugaban Somalia ya tsawaita wa kansa wa'adin mulki

Shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Mohamed ya rattaba hannu kan wata doka mai sarkakiya da zummar tsawaita wa kansa wa’adin mulkinsa da shekaru biyu duk da barazanar da kasashen duniya suka yi masa na kakaba masa takunkumi.

Shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo
Shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo Reuters/Feisal Omar
Talla

Gidan rediyon gwamnatin Somalia da ke birnin Mogadishu ya ce, shugaban da ake yi wa lakabi da Farmajo ya sanya hannu kan kudirin dokar mai kula da lamurran zabe a kasar bayan samun amincewar Majalisar Wakilai kadai.

A ranar Litinin ne Majalisar Wakilan ta Somalia ta kada kuri’ar tsawaita wa Farmajo wa’adin mulkinsa wanda ya kamata ya kare a cikin watan Fabairu bayan kwashe tsawon watanni ana kiki-kaka kan gudanar da zabe a kasar mai fama da tashin hankali.

Sai dai  Majalisar Dattawan  Kasar ta caccaki matakin na Farmajo wanda ta bayyana a matsayin karan-tsaye ga  kundin tsarin mulki, tana mai cewa, sam ba a gabatar da kudirin dokar ba a gabanta don samun amincewarta kamar yadda doka ta tsara.

Shugaban Majalisar Dattawan, Abdi Hashi Abdullahi ya ce, wannan matakin zai jefa Somalia cikin rikicin siyasa da tabarbarewar tsaro.

Tuni Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Afrika da Kungiyar Tarayyar Turai suka bayyana damuwarsu kan wannan al’amari.

Kasashen duniya sun ci gaba da kiraye-kirayen ganin an gudanar da zabe a kasar kamar yadda shugbannin kasar  suka amince a wani zama da suka yi a cikin watan Satumba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.