Isa ga babban shafi

Somalia: Al-Shabaab ta kai hari a kauyukan da ke kusa da iyakar Habasha

Wasu ‘yan tada kayar bayan kungiyar al-Shabaab ta Somaliya sun kai hari a wasu kauyuka biyu da ke kusa da kan iyaka da Habasha, inda suka kashe jami’an ‘yan sandan Habasha 17 a cikin yankin Somaliya yayin da aka kashe mayakanta 63.

Tun a shekara ta 2007, kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaeda, ke fafutukar hambarar da gwamnatin da ke samun goyon bayan kasashen duniya a Somaliya.
Tun a shekara ta 2007, kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaeda, ke fafutukar hambarar da gwamnatin da ke samun goyon bayan kasashen duniya a Somaliya. AFP/File
Talla

Harin da ba kasafai ake kaiwa kan iyakar ba ya auku ne a ranar Laraba lokacin da mayakan kungiyar da ke da alaka da al Qaeda suka kai farmaki a kauyukan Yeed da Aato da ke yankin Bakool na Somaliya bayan kashe wani kwamandojinsu da aka yi kwanaki a kan iyakar Habasha, acewar wani kwamandan Habasha da ya nemi a sakaya sunansa saboda baida izinin Magana da manema labarai.

Ba kasafai kungiyar al Shabaab ke kai wa a yankunan da ke kusa da kan iyakar Habasha hari ba, saboda karfin tsaron da Habasha ke da shi a yankin dake karkashin kulawar dakarun wanzar da zaman lafiya na Afirka.

Wani kwamandan kungiyar Al Shabaab ya tsallaka kan iyaka ne don samar da wata runduna a Habasha, in ji kwamandan Habashan, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana da manema labarai.

Ya ce 'yan sandan yankin Habasha sun kwace manyan bindigogi da motoci daga hannun mayakan al Shabaab.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.