Isa ga babban shafi

Nakasassu ma basu tsira daga zaluncin sojoji da 'yan tawayen Habasha ba - Rahoto

Hukumar kare hakkin dan Adam mai zaman kanta a Habasha, ta ce ‘yan kasar sun fuskanci matsanancin zalunci, da rashin tausayi daga sojojin gwamnati da kungiyoyin 'yan tawaye.

Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da suke tsere daga muhallansu saboda rikicin yankin Tigray.
Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da suke tsere daga muhallansu saboda rikicin yankin Tigray. AP - Nariman El-Mofty
Talla

A rahotonta na baya-bayan nan hukumar, ta tattara laifukan cin zarafin da suka hada da kisan gilla da nuna kabilanci da kuma aikata fyade a cikin watanni 12 zuwa Yunin da ya gabata a sassan kasar ta dake zama ta biyu mafi yawan al'umma a Afirka.

Hukumar ta kara da cewa hatta mata, yara da tsofaffi da kuma nakasassu basu a tsira da rayukansu ba.

Karo na farko kenan da hukumar kare hakkin dan Adam ta Habasha ke fitar da rahoton shekara, tun bayan nada Daniel Bekele, tsohon mai ba da shawara ga Amnesty International a matsayin shugabanta a shekarar 2019.

Kasar Habasha na fuskantar rashin zaman lafiya a yankuna da dama, musamman yankin Tigray inda dakarun gwamnati ke gwabza kazamin fada da kungiyar 'yan tawayen TPLF tun watan Nuwamban shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.