Sojojin Habasha sun kona wani dan kabilar Tigrai da ransa
Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta kasar Habasha ta ce dakarun gwamnati ne suka kone wani dan kabilar Tigray da ransa har lahira, cikin wani faifan bidiyo da ya yadu ta shafukan sada zumunta, abinda ya janyo cece-kuce a ciki da wajen kasar.
Wallafawa ranar:
A ranar Asabar ne gwamnatin Habasha ta sha alwashin gudanar da bincike tare da daukar mataki kan duk wanda ke da hannu a cikin ta’addancin, wanda faifan bidiyon da aka yada ya nuna yadda wasu mutane da suka hada da masu sanye da kakin soji ke yi wa mutumin da aka kashe ba'a, kafin daga bisani su cinna masa wuta.
Wannan danyen aikin ya afku ne a ranar 3 ga watan Maris da muke, a yankin Benishangul Gumuz da ke arewa maso yammacin kasar mai iyaka da Sudan da Sudan ta Kudu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu