Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Habasha ta sanar da yin afuwa ga fitattun 'yan adawa da 'yan tawayen TPLF

Gwamnatin Habasha ta sanar da yin afuwa ga wasu manyan fursunonin siyasa ciki har da manyan 'yan tawayen TPLF na yankin Tigray, a wani yunkuri na karfafa shirin babban taron warware matsalolin kasar.

Fira Ministan kasar Habasha Abiy Ahmed
Fira Ministan kasar Habasha Abiy Ahmed REUTERS/Kumera Gemechu
Talla

Matakin na ba-zata ya zo ne bayan da aka samu lafawar yakin da aka kwashe akalla watanni 14 ana gwabzawa tsakanin sojojin Habasha da ‘yan tawayen TPLF a yankin Tigray inda sojojin gwamnati suka sake kwace wasu muhimman garuruwa, yayin da kuma mayakan suka janye zuwa sansaninsu dake yankin na arewacin Habasha.

Daga jerin wadanda gwamnatin Habashan ta yi wa afuwa dai, akwai fitattun myakan kungiyar TPLF da kuma shugabannin ‘yan adawa na Oromo, kabila mafi girma a Habasha, da kuma na yankin Amhara.

Sai dai, babu karin bayani kan ko an fara sakin mutanen da aka yi wa afuwar siyasar.

Firayim Minista Abiy Ahmed da ya samu lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel, wanda kuma ya je fagen fama a watan Nuwamban da ya gabata don jagorantar dakarunsa a yaki da ‘yan tawayen kasar, shi ma ya yi kira da a yi sulhu da hadin kai, a cikin wata sanarwa da ya fitar yayin bikin Kirsimeti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.