Isa ga babban shafi
Habasha -Tigray

Gwamnatin Habasha ta yi ikirarin kwato garuruwa daga hannun 'yan tawaye

Gwamnatin Habasha ta ce dakarunta sun yi nasarar kwato garuruwa da dama daga hannun 'yan tawayen TPLF a yankin Tigray, da suka hada da Kobo da Woldiya a arewacin kasar, bayan kazamin fadan da aka gwabza a yakin da kawo yanzu aka shafe watanni 13 ana yi, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.

Sojojin kasar Habasha a kusa da birnin Humera.
Sojojin kasar Habasha a kusa da birnin Humera. EDUARDO SOTERAS AFP
Talla

An dai katse hanyoyin sadarwa a yankin na Tigray tare da hana ‘yan jarida damar shigarsa, abin da ya sa da wuya a iya tantance ikirarin da bangarorin dake fada da juna ke yi.

A baya bayan nan, hukumar kare hakkin dan Adam ta Majlisar Dinkin Duniya ta amince da tura tawagar masu bincike zuwa arewacin Habasha, domin tantance zarge-zargen aikata laifukan yaki a tsakanin dakarun kasar da mayakan ‘yan tawaye, musamman ma kan cin zarafi da ake zargin yi wa mata.

Tun daga karshen watan Oktoba, bangaren gwamnati da na ‘yan tawaye ke ikirarin samun nasarar mamaye karin yankuna a arewacin Habasha.

A ranar Lahadin da ta gabata ‘yan tawayen TPLF suka sake kwace garin Lalibela da ke kunshe da wurin tarihi na hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya, kwanaki 11 bayan da dakarun Habasha suka yi ikirarin kwace garin daga hannun ‘yan tawayen.

A watan Nuwamban shekarar 2020 yaki ya barke a Tigray, bayan da Firaminista Abiy Ahmed ya aika da sojoji zuwa yankin da ke arewacin kasar, domin kawar da kungiyar ta TPLF, da ya zarga da kai hare-hare kan sansanonin sojoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.