Isa ga babban shafi
Habasha-Tigray

'Yan tawayen Tigray sun kwace iko da garin Lalibela na Habasha

‘Yan tawayen Tigray sun sake kwace garin Lalibela da ke yankin arewacin Habasha, garin da ke dauke da wuraren tarihin da ke karkashin kulawar hukumar Ilimi da al’adu ta majalisar dinkin duniya, wato UNESCO.

Wani yanki na garin Lalibella.
Wani yanki na garin Lalibella. Solan KOLLI AFP
Talla

‘Yan tawayen na Tigray sun sake karbe wannan gari mai dimbin tarihi ne, kwanaki 11 bayan garin ya koma hannun dakarun gwamnati.

Nasarar da ‘yan tawayen suka samu, na matsayin sabon babi na watanni 13 da aka kwashe ana rikici a yankin na Tigray, inda dubban mutane suka rasa rayukansu , yayin da wasu da dama suka rasa muhallansu .

Wani mazaunin yankin ya shaidawa kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, yanzu haka mayakan na Tigray sun yi kane-kane a cikin garin na Lalibela, amma kawo yanzu an dakatar da dauki ba dadi.

Sai dai tuni da dama daga cikin mazauna garin suka fice zuwa tudun mun tsira saboda fargabar abin da ka iya biyo baya da zarar sojojin gwamnati sun dawo domin daukar fansa.

Wannan gari na Lalibela na da tazarar kilomita 645 daga babban birnin kasar Adisa Baba , yayinda ya ke dauke da majami'u 11 da aka gina cikin koguna shekaru kalilan bayan haihuwar Annabi Isa, inda kuma  Kiristoci daga sassan duniya ke ziyartar garin a duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.