Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Eritrea da Habasha sun yi tir da takunkuman Amurka kan rikicin Tigray

Kasashen Eritrea da Habasha sun yi tir da takunkuman da Amurka kakabawa  sojojin da kuma gwamnatin Eritrea, amatsayin matsin lamba da Amurka ke yi kan masu ruwa da tsaki a rikicin yankin Tigray da kuma samar da zaman lafiya a wannan yanki na arewacin Habasha.

Firanminitsan Habasha Abiy Ahmed, (hagu) da shugaban kasar Eretria (dama) Isaias Afwerki.
Firanminitsan Habasha Abiy Ahmed, (hagu) da shugaban kasar Eretria (dama) Isaias Afwerki. AFP/File
Talla

Eritrea ta caccaki Amurka kan kakaba wa kasar sabbin takunkumai, sakamakon kazamin rikici a makwabciyarta Habasha, tana mai kiran matakin da cewa haramtatce ne kuma rashin da'a ce.

Itama kasar Habasha ta yi Allah-wadai da sabbin takunkuman, inda ta yi kira ga Washington da ta yi watsi da matakin da ta dauka.

Matakan da Amurka ta sanar tun ranar Juma'a sun zo ne a matsayin martani ga matakin da Eritrea ta dauka na tura dakaru zuwa yankin Tigray na kasar Habasha domin marawa Firanminista Abiy Ahmed baya a yakin da ake yi da kungiyar 'yan tawayen Tigray People's Liberation Front (TPLF).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.