Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Fira Ministan Habasha ya bukaci sadaukarwa don ceto kasar daga 'yan tawaye

Fira Ministan Habasha ya bukaci ‘yan kasarsa da su kasance cikin shirin sadaukar da rayukansu da ceton kasar daga barazanar tsaron da take fuskanta.

Fira Ministan kasar Habasha Abiy Ahmed, a birnin Addis Ababa.
Fira Ministan kasar Habasha Abiy Ahmed, a birnin Addis Ababa. Amanuel Sileshi AFP/Archivos
Talla

Kiran na Abiy Ahmed ya zo ne a yayin da fada a arewacin kasar ke kara kamari tsakanin sojojin gwamnati da ‘yan tawayen Tigray wadanda ke barazanar mamaye babban birnin kasar Addis Ababa nan da ‘yan kwanaki.

Sanarwar tasa ta zo ne kwana guda bayan da kungiyoyin ‘yan tawaye 9 suka ce za su hada karfi da karfe wajen marawa kungiyar ‘yan tawayen TPLF na yankin Tigray baya, wadda ta shafe shekara guda tana yaki da gwamnatin Habasha.

A baya bayan nan ne dai Amurka ta baiwa jami’an diflomasiyyar ta da aikinsu baya da muhimmanci umarnin ficewa daga Habasha, yayin da yakin da ake gwabzawa tsakanin ‘yan tawayen Tigray da dakarun gwamnati ke kara yin kamari.

A daren ranar Juma’a ne dai ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ba da umarnin cikin sabuwar manhajar tafiye-tafiyen da ta fitar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.