Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Amurka ta bukaci 'yan kasar ta su gaggauta ficewa daga Habasha

Amurka ta bukaci ‘yan kasar ta da su gaggauta ficewa daga sassan Habasha a dai dai lokacin da kungiyoyin ‘yan tawaye da dama suka sanar da kulla kawance da juna a wani yunkuri na hada karfi dpn afkawa birnin Adis Ababa da ke matsayin fadar gwamnatin kasar.

Shugaba Joe Biden na Amurka.
Shugaba Joe Biden na Amurka. REUTERS - KEVIN LAMARQUE
Talla

Ana ci gaba da fargaba a sassan birnin na Addis Ababa wanda ya tilastawa wasu daidaikun fararen hula fara ficewa daga birnin dai dai lokacin da ‘yan tawayen ne Tigray ke ci gaba da matsawa gab da babban birnin, lamarin da ke tabbatar da yiwuwar iya samun kazamar gwabzawa tsakanin 'yan tawayen da dakarun gwamnati.

A kiran da Amurkan ta yi da yammacin yau juma'a ta bukaci mutanenta da ke kowanne yanki na kasar su gaggauta ficewa don kaucewa rikicin da ka iya barkewa a kasar ta nahiyar Afrika matakin da ke zuwa bayan kawancen Oromo da 'yan tawayen TPL na yankin Tigray wadanda ke da nufin hada karfi don afkawa dakarun gwamnati.

Tun a shekaranjiya laraba ne ‘yan tawayen suka kwace birnin Kemissie da ke lardin Amhara mai tazarar kilomita 325 a arewacin birnin na Adis Ababa, lamarin da ke kara sanya fargaba dangane da makomar kasar.

Tuni Firaminista Abiy Ahmed ya sanar da kafa dokar ta baci a fadin kasar, tare da yin kira ga Al'ummar kasar da su kasance cikin shirin kare kasar daga wadanda ya bayyana su a matsayin makiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.