Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Rikicin Habasha na neman dagula lissafin shugabannin gabashin Afirka

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya kira taron shugabannin kungiyar kasashen gabashin Afirka a ranar 16 ga watan Nuwamba, domin tattaunawa kan rikicin kasar Habasha.

Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni, a birnin Kampala.
Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni, a birnin Kampala. Badru KATUMBA AFP/Archivos
Talla

Kiran dai ya zo ne a yayin da fadan da ake gwabzawa tsakanin ‘yan tawayen TPLF da dakarun gwamnati a yankin Tigray ke dada yin kamari.

Shugaban na Uganda yayi wannan kira ne a Alhamis din nan, inda karamin ministan harkokin wajen kasar Okello Oryem ya ce tuni Museveni ya fara tuntubar Fira Minista Abiy Ahmed game da halin da ake ciki a Habasha, gami da bayyana damuwa kan kin amincewar da ‘yan tawayen TPLF na yankin Tigray suka yi dangane da neman tsagaita bude wuta.

Yanzu haka dai akwai fargabar ‘yan tawayen na Tigray na iya mamaye birnin Addis Ababa cikin ‘yan watanni ko makwanni masu zuwa kamar yadda wata kungiyar Oromo da ke kawance da mayakan Tigray ta bayyana.

Wasu mayakan 'yan tawayen Tigray a birnin Makele dake arewacin kasar Habasha.
Wasu mayakan 'yan tawayen Tigray a birnin Makele dake arewacin kasar Habasha. AFP - YASUYOSHI CHIBA

‘Yan tawayen na kungiyar Tigray People's Liberation Front da suka shafe shekara guda suna yakar gwamnatin Firaiminista Abiy Ahmed, sun yi ikirarin samun gagarumar nasarar mamaye wasu yankuna a 'yan kwanakin nan, tare da taimakon kawayenta na 'yan tawayen Oromo Liberation Army (OLA).

Tuni dai gwamnatin Habasha ta ayyana dokar ta baci a dukkanin fadin kasar a ranar tare da bada umurni ga mazauna birnin Addis Ababa da su shirya don kare matsugunan su.

A karkashin dokar ta-baci, hukumomi na iya daukar duk wani dan kasa da shekarunsa ya kai ga aikin soji, tare da dakatar da duk wata kafar yada labarai da aka yi zargin tana goyon bayan ‘yan tawayen yankin Tigray kai tsaye ko kuma a fakaice.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.