Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Habasha ta kaddamar da harin sama a kan 'yan tawayen Tigray

Dakarun Habasha sun kaddamar da  wasu hare hare ta sama har 2 a ranar Lahadi a kan wuraren  da wani jami’in gwamnati  ya bayyana a matsayin sansanonin ‘yan tawaye a Tigray, hare hare na  7 da 8 a yankin arewacin kasar da yaki ya daidaita a cikin mako daya.

Map showing the Tigray region of Ethiopia
Map showing the Tigray region of Ethiopia AFP/File
Talla

Hare haren da ke nesa da babban birnin yankin, wato Makele, na nuni da yadda sojin gwamnati ke fadada dirar mikiyar da ta ke yi ta sama, wanda ya janyo caccaka daga kasashen duniya.

Babu wani martani daga kungiyar ‘yan tawaye ta TPFL, wadda ta bayyana hare haren da aka kai ta sama tun da farko a matsayin shaidar cewa gwamnatin kasar ba ta daraja rayukan farar hula.

Zalika, babu wani bayani a game da wadanda hare haren suka rutsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.