Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Sojin Habasha sun kaddamar da hare-hare a yankin Tigray

'Yan tawayen yankin Tigray na Habasha sun zargi sojojin kasar da kaddamar da mabanbantan hare-hare ta kasa a kusan kowanne sashe na yankin ciki har da Amhara duk kuwa da lafawar rikicin da yankin ke gani tsawon watanni.

Yankin Tigray na Habasha.
Yankin Tigray na Habasha. © Stringer/File Photo/Reuters
Talla

Sanarwar da ‘yan tawayen na Tigray ko kuma TPLF suka fitar ta ce hare-haren Sojin Habashan ya faru da sanyin safiyar jiya litinin ko da yak e babu alkaluman wadanda suka mutu ko kuma suka jikkata a mabanbantan farmakin.

Duk da tarin zarge-zargen farmakin Sojin tare da take hakkin dan adama a yankin na Tigray har zuwa yanzu ofishin firaminista Abiy Ahmed bai tabbatar da hare-haren ba sai dai ya nanata kudirin gwamnatin na bayar da cikakkiyar kariya ga al'ummar kasar ga 'yan tawayen.

Kungiyar 'yan tawayen na Tigray na zargin firaminista Abiy Ahmad da kokarin sake mamaye yankin ta hanyar girke tarin motocin yaki da manyan makamai don kaluablantar mayakan 'yan tawayen na TPLF da tuni gwamnatin kasar ta ayyana su a matsayin 'yan tawaye.

Gwamnatin Abiy ta jaddada cewa ayyukan soji a arewacin kasar na kaiwa ‘yan tawaye hari, wanda a hukumance ta ayyana kungiyar a matsayin ta ‘yan ta'adda, babu gudu ba ja da baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.