Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Majalisar Dinkin Duniya ta soke zirga -zirgar jiragen sama yankin Tigray na Habasha

Sabbin hare-hare ta sama da Habasha ta kai  babban birnin yankin Tigray a ranar Juma'a sun jikkata fararen hula 11 tare da tilastawa wani jirgin Majalisar Dinkin Duniya juyawa  daga yankin da ke fama da yunwa.

Yankin Tigray na kasar Habasha na fama da matsanaicin yunwa.
Yankin Tigray na kasar Habasha na fama da matsanaicin yunwa. Amanuel Sileshi AFP
Talla

Lamarin dai ya sa Majalisar Dinkin Duniya dakatar da jigilar fasinjoji da take yi zuwa yankin Tigray sau biyu a mako domin taimakawa ma'aikatan agaji, kamar yadda kakakin MDD Stephane Dujarric ya shaida wa manema labarai.

Hare-haren na sama, sune na biyar da aka kaiwa birnin tun daga ranar Litinin a cewar gwamnati, wanda ke zuwa daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada a kudancin yankin Amhara yayin da yakin Habasha na kusan shekara guda ke kara kamari.

Mai magana da yawun Franminista Abiy Ahmed, Billene Seyoum, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa sojojin saman sun kai hari kan wata cibiyar horas da kungiyar 'yan tawayen Tigray (TPLF) ke amfani da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.