Isa ga babban shafi
hAKKIN MATA

MDD ta bukaci kasashe su kara kaimi wajen kare hakkin Mata

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nemi kasashen duniya da su kara kaimi wajen kare hakkin mata, a dai-dai lokacin da ake ganin an samu koma baya ga shirin kare hakkokin mata a Afghanistan da ke karkashin ikon Taliban da sauran wurare a duniya.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres.
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Guterres ya shaidawa kwamitin sulhu cewa  bisa alamun da ke akwai an samu koma baya sosai wajen kare hakkokin mata, musamman yara mata, don haka akwai bukatar kare ‘yancinsu.

Sakatare Janar na MDD ya nanata cewa a yanzu kam ba za su lamunci cin zarafin mata daga kowanne bangare ba, kuma abin da yafi kamata a yi shine jajircewa wajen basu kariya a kasashen da ke fama da yake-yake.

MDD ta ce a kasashen Myanmar, Habasha, Yemen da sauran sassan duniya ana tauye hakkin mata ko kuma ma kawar da su daga doron kasa, kuma haka abin yake a kasar Mali da ke nahiyar Afirka, tun bayan juyin mulki biyu cikin watanni tara da aka yi a kasar, yancin mata ya samu koma baya sosai.

A Afghanistan, kuwa 'yan mata da mata abin da suka ci karo da shi shine batun take musu hakkokinsu, bayan fafutukar da suka dauki tsawon shekaru suna yi, ciki kuwa har da ' yancinsu na zuwa makaranta.

Tun lokacin da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Taliban ta kwace mulki a karshen watan Agusta, ta hana 'yan mata komawa makarantar sakandare yayin da ta umarci samari su koma karatu.

A Afghanistan, Gutteres ya ce, Majalisar Dinkin Duniya tana ci gaba da ba da gudummawa, kuma za ta ci gaba da inganta shirinta na kare hakkokin iyaye mata da 'yan mata a duk mu'amalarsu da hukumomin Taliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.