Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Habasha ta zargi 'yan tawayen Tigray da kisan matasa 100 a Kombolcha

Gwamnatin Habasha ta ce ‘yan tawayen kungiyar TPLF da ke yankin Tigray, sun kashe matasa akalla dari daya  a farmakin da suka kai garin Kombolcha da ke arewacin kasar karshen makon da ya gabata.

Mayakan 'yan tawayen Tigray na Habasha bayan kwace iko da Mekele cikin watan Yuni.
Mayakan 'yan tawayen Tigray na Habasha bayan kwace iko da Mekele cikin watan Yuni. Yasuyoshi Chiba AFP/File
Talla

Zargin kisan, na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnatin kasar ta Habasha ta fitar a wannan litinin, bayan da ‘yan tawayen suka yi nasarar kwace birane biyu ciki har da Kombolcha a karshen makon jiya.

Sanarwar gwamnati ta ce bai kamata kasashen duniya su kawar da kai a game da tu’annantin da ‘yan tawayen na Tigray ke aikatawa kan fararen hula a garuruwan da suka kwace daga hannun dakarun gwamnatin kasar ba.

Lokacin da kamfanin dillancin labaran Reuters ya nemi jin ta bakin kakakin ‘yan tawayen Getachew Reda dangane da wannan zargi da gwamnati ke yi masu, ya ki ya ce uffan dangane da hakan.

A cikin kwanaki biyu da suka gabata, ‘yan tawayen kungiyar ta TPLF sun kwace birane biyu daga hannun dakarun gwamnati, da suka hada da Kombolcha da kuma Dessie da ke arewacin kasar ta Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.