Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Mutane 10 sun mutu sakamakon luguden wuta da Habasha ke yi a Tigray

Sojin Habasha na ta ci gaba da luguden wuta ta sama kan ‘yan tawaye dake yankin Tigray na kasar, inda majiyoyi masu tushe ke  cewa rayukan mutane 10 aka salwantar a Alhamis kawai.

Taswirar Habasha da ke nuna yankin Tigray
Taswirar Habasha da ke nuna yankin Tigray AFP
Talla

A cewar Gwamnatin kasar, hare-haren ta sama ta kai shi ne a wata masana’anta dake Mekele inda ‘yan kungiyar ‘Yantar da al’ummar Tigray wato Tigray Peoples Liberation Front TPLF,  ke amfani da shi.

Dr Hayelom Kebede  , Daraktan a asibitin Ayder dake  Mekele ya ce harin ya shafi asibitin, kuma an yi barna, domin mutane 10 sun mutu  wasu 21 kuma suka sami raunuka.

Ma’aikatar harkokin sadarwa na yankin Tigray ta ce a na ta  bangaren an sami barna a rukunin gidajen kwana na ma’aikata.

Tun da fari kakakin kungiyar ta ‘yantar da al’ummar Tigray, ta hannun kakakinta Getachew Reda  ta sanar da cewa  lallai sun yi hasarar rayukan mutane a harin da sojan Habashan suka kai ta sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.