Isa ga babban shafi
Habasha -Tigray

An kame ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya fiye da 10 a Habasha

Jami'an tsaron Habasha sun kame ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya fiye da 12 dake aiki a kasar, kamar yadda jami'an agaji suka tabbatar.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. Javier Soriano AFP
Talla

Bayanai sun ce an kame jami’an ne a birnin Addis Ababa, yayin wani samame da aka kaiwa 'yan kabilar Tigray a karkashin dokar ta baci.

Daya daga cikin majiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da suka tsegunta labarin kame, ta ce an dauke wasu daga cikin jami’an da aka kame ne a gidajensu.

Tuni dai wata mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya a Geneva ta sanar da mika bukatar sakin jami’an nasu ga ma'aikatar harkokin wajen kasar Habasha.

A makon da ya kare, gwamnatin Fira Minista Abiy Ahmed ta sanar da kafa dokar ta-baci ta tsawon watanni shida a fadin Habasha, sakamakon fargabar da ake yi na cewa mayakan kungiyar ‘yan tawayen Tigray People’s Liberation Front wato TPLF a Turance da kungiyar ‘yan tawayen Oromo Liberation Army OLA za su iya kutsawa babban birnin kasar.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama ciki har da Amnesty International dai sun yi Allah wadai da dokar ta bacin, wadda ke ba da damar bincikar duk wanda ake zargi da tallafawa kungiyoyin ta'addanci tare da tsare shi ba tare da izini ba.

Ana dai takun saka tsakanin gwamnatin Fira Minista Abiy da Majalisar Dinkin Duniya a tsawon lokacin da aka shafe ana gwabza yaki sojojin gwamnati da ‘yan tawayen TPLF, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, tare da jefa wasu dubban cikin mummunan yanayi na yunwa.

A karshen watan Satumba ma'aikatar harkokin wajen Habasha ta sanar da korar wasu manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya bakwai saboda katsalandan cikin harkokin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.