Al'ummar Tigray na fama da matsanancin karancin abinci- rahoto
Rahotanni daga yankin Tigray na Habasha na nuna yadda yanzu haka al’umma ke fuskantar tsananin kamfar abinci da man fetur dai dai lokacin da gwamnati ke sake tsananta dokar ta baci a sassan kasar musamman birnin Merkele.
Wallafawa ranar:
Wani rahoto da Majalisar dinkin Duniya ta fitar kan rikicin na Habasha ya nuna cewa har zuwa yanzu motoci kalilan ne ke iya zirga-zirga a titunan Makele duk da kasancewar birnin mai yawan cikowar jama’a a baya.
Acewar rahoton baya ga karancin man fetur da kuma kamfar abincin da yankin ke fuskantar akwai kuma hauhawar farashin kayakin masarufi wanda yasa galibin mutane gaza iya ciyar da iyalansu.
Shaidun gani da ido sun ce gwamnatin Habasha ta dakatar da duk wani kayakin dauki ga yankin wanda ya sanya jama’a rayuwa a tsananin wahala yayinda was uke ci gaba da tserewa don samun sa’ida.
Mayakan ‘yan tawayen yankin na Tigray dai na ci gaba da zafafa farmaki tare da kalubalantar gwamnatin Abiy Ahmed inda shugabancinta ya yi ikirarin samun gagarumar nasara kan dakarun gwamnati dai dai lokacin da suke gab da isa Addis Ababa babban birnin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu