Isa ga babban shafi
Habasa-MDD

MDD ta dakatar da rabon abinci a Tigray bayan wawason jama'a

Hukumar samar da abinci ta duniya ta dakatar da rabon kayan agaji a garin Kombolcha da ke arewacin kasar Habasha, bayan da aka wawure kayayyakin da ta adana, al’amarin da ake zargin ‘yan tawayen Tigray da wasu mutanen yankin da aikatawa.

Dubban mutane ke fama da Yunwa a yankin na Tigray tun bayan faro yaki fiye da shekara guda.
Dubban mutane ke fama da Yunwa a yankin na Tigray tun bayan faro yaki fiye da shekara guda. Yasuyoshi CHIBA AFP/File
Talla

Stephane Dujarric ya shaidawa manema labarai cewa, an wawashe kayan abinci masu yawa da suka hada da kayan abinci masu gina jiki ga yara masu fama da tamowa, inda ya yi gargadin cewa sace-sacen na da nasaba da karuwar karancin abinci a arewacin Habasha.

Ya ce a lardunan Tigray, Amhara da Afar, kimanin mutane miliyan 9.4 a yanzu suna cikin tsananin bukatar agajin abinci.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum miliyan 5.2 daga cikinsu suna yankin Tigray, inda 534,000 ke a lardin Afar sai kuma miliyan 3.7 da kelardin Amhara.

A cewar MDD barazanar da ma’aikatanta suka fuskanta a yankin, ya sa aka yanke shawarar dakatar da rabon kayan abinci a Dessie da Kombolcha, garuruwa biyu masu muhimmanci kan hanyar zuwa babban birnin kasar, Addis Ababa, tana mai jaddada cewa irin wannan cin zarafi na jami'an jin kai da sojoji ke yi ba abu ne da za a amince da shi ba.

A baya-bayan nan ne dai gwamnatin Habasha ta sanar da cewa ta kwato garuruwan biyu, sai dai sojojin na Tigray sun ce sojojin sun kwato yankunan bayan da 'yan tawayen suka fice.

Yakin dai ya barke ne a watan Nuwamban shekarar 2020 lokacin da Firayim Minista Abiy Ahmed ya aika da sojoji zuwa yankin Tigray domin su hambarar da kungiyar ‘yan tawayen kabilar Tigrai matakin da ya ce ya zo ne a matsayin martani ga hare-haren ‘yan tawaye a sansanonin sojoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.