Kungiyar kare hakkin dan adam na zargin 'yan tawayen Tigray da laifukan yaki
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce sojojin Eritrea da ‘yan tawayen Tigray sun aikata muggan laifukan da suka hada da fyade kisan gilla, da kuma azabatar da 'yan gudun hijirar Eritrea a yankin Tigray da ke arewacin Habasha, yayin hare-haren da masu rajin kare hakkin dan adam suka bayyana a matsayin laifukan yaki.
Wallafawa ranar:
Rahoton da Human Rights Watch ta fitar a ranar Alhamis ya ce dakarun na Eritrea da ‘yan tawayen TPLF sun aikata laifukan yakin ne yayin hare -hare da suka kai kan wasu sansanonin ‘yan gudun hijira biyu a yankin Tigray.
Kawo yanzu dai Eritrea ba ta ce komai kan zargin da ake yiwa dakarun na ta ba, sai dai a baya ta sha musanta irin wannan tuhuma kan sojojin nata, kan cin zarafin fararen hula.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu