Isa ga babban shafi
AU - TIGRAY

'Yan tawayen Tigray na adawa da nadin Obasanjo a matsayin mai shiga tsakani

'Yan tawayen yankin Tigray na kasar Habasha da ke fama da rikici sun zargi kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da nuna son kai, kwanaki bayan da kungiyar ta nada tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a matsayin mai shiga tsakani a rikicin da aka shafe watanni ana yi.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yayin ziyara aiki a Goma dake gabashin Congo, 15/11/2008
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yayin ziyara aiki a Goma dake gabashin Congo, 15/11/2008 AP - Jerome Delay
Talla

Mai magana da yawun kungiyar 'yan tawayen Tigray (TPLF), Getachew Reda, ya zargi AU da "nuna son kai" wajen fifita gwamnatin Habasha, kuma ya ce zai yi wuya manzannin su sauke nauyin su.

Arewacin Habasha na fama da tashe -tashen hankula tun daga watan Nuwamba, lokacin da Firayim Minista Abiy Ahmed ya tura sojoji zuwa Tigray don fatattakar TPLF, jam'iyyar da ke mulkin yankin, yana mai cewa matakin ya zo ne a matsayin martani ga hare -haren da aka kai kan sansanin sojojin gwamnati.

Wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel ta shekarar 2019 ya yi alkawarin samun nasara cikin sauri, amma a maimakon haka yakin ya ci gaba har na tsawon watanni, lamarin da ya haifar da matsalar jin kai a Tigray, yayin da 'yan tawayen suka shiga yankunan makwabta na Afar da Amhara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.