Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Rikicin Tigray: Firaministan Habasha zai dauki sabbin sojoji miliyan 1

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya bayyana shirin gwamnatinsa na daukar sabbin sojoji miliyan 1 a wani yunkuri na magance matsalar tsaron da kasar ke fama da shi.

Firaministan Habasha Abiy Ahmed a gaban zauren majalisar dokokin kasar.
Firaministan Habasha Abiy Ahmed a gaban zauren majalisar dokokin kasar. © AFP - AMANUEL SILESHI
Talla

Matakin daukar sabbin Sojojin dubu 1 da Firaminista Abiy Ahmed wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a 2019 ya sanar, na zuwa mako guda bayan da ‘yan tawayen TDF da ke fafutukar ganin ballewar yankin Tigray suka kwace iko da Mekele babban birnin yankin gabanin tsagaita wuta a rikicin.

Watanni 8 kenan ana fama da yaki tsakanin ‘yan tawayen na TDF da kuma dakarun gwamnatin Habasha a yankin na Tigray, yakin da ya tagayyara iyalai da dama baya ga haddasa asarar dimbin rayuka daga bangarorin biyu.

Rikicin yankin Tigray na cigaba da daukar hankalin duniya tun bayan barkewarsa a watan Nuwamban shekarar 2020.
Rikicin yankin Tigray na cigaba da daukar hankalin duniya tun bayan barkewarsa a watan Nuwamban shekarar 2020. Yasuyoshi Chiba AFP

Da ya ke jawabi gaban majalisar kasar, Abiy Ahmed ya ce cikin makwanni 3 masu zuwa za a horar da dakaru na musamman dubu 100 da za su tunkari barazanar tsaron da kasar ke fuskanta.

Tun bayan da TDF ta sanar da kwace iko da Mekele da sauran kananun garuruwan da ke yankin arewacin kasar, Habasha ta janye dakarunta tare da amincewa da shirin tsagaita wuta.

A cewar Firaministan, baya ga dakarun na musamman akwai kuma bukatar sojin sa kai wadanda suma za a horar da rabin miliyan nan da watanni 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.