Habasha ta yi watsi da zargin hana kungiyoyin agaji shiga yankin Tigray
Gwamnatin Habasha ta yi watsi da zargin da ake mata na cewa tana shirin haramtawa kungiyoyin agaji shiga yankin Tigray mai fama da rikici don tallafawa wadanda yaki ya tagayyara.
Wallafawa ranar:
Wannan zargi ya bijiro ne kwanaki 2 bayan lalata wasu muhimman gadoji da suke zaman manyan hanyoyin shigar da kayayyakin agaji zuwa yankin na Tigray.
A makon nan dake shirin karewa ne dai mayakan ‘yan tawayen TPLF suka yi bazata wajen sake kwace iko da Makele babban birnin yankin, bayan shafe watanni 8 suna gwabza fada sojojin Habasha dake kokarin murkushe su.
Wani rahoton hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya WFP, ya ce mutane akalla miliyan 5 da dubu 200 dake zaman kashi 91 cikin 100 na al’ummar yankin Tigray na cikin bukatar agajin gaggawa na kayayyakin abinci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu