Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Farmakin jiragen yakin Habasha kan kasuwa a Tigray ya kashe mutane 64

Jami’an lafiya a Habasha sun ce mutane akalla 64 sun rasa rayukansu, a yayin da wasu 180 suka jikkata, sakamakon farmakin da jiragen yakin Habasha suka kai kan wata kasuwa dake yankin Tigray mai fama da rikicin ‘yan tawaye.

Wasu 'yan kasar Habasha yayin kokarin tserewa daga yankin Tigray zuwa cikin Sudan. 1/12/2020.
Wasu 'yan kasar Habasha yayin kokarin tserewa daga yankin Tigray zuwa cikin Sudan. 1/12/2020. © REUTERS - BAZ RATNER
Talla

Yayin tabbatar da kai harin, mai baiwa gwamnatin yankin Tigray shawara kan kula da lafiyar mata da kananan yara Mulu Atsbaha, ya zargi sojojin Habasha da yiwa fararen hula kisan gilla da gangan a garin Togoga mai nisan akalla kilomita 20 daga Makele babban birnin yankin.

Sai dai kakakin rundunar sojin kasar ta Habasha Kanal Getnet Adane yayi watsi da zargin, inda ya ce dukkanin mutanen da suka halaka a kasuwar garin na Togoga, mayakan ‘yan tawaye ne sanye da rigunan fararen hula.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gudanar da bincike kan farmakin jiragen yakin na Habasha, wanda ya zo a yayin da ake kidayar kuri’un zaben ‘yan majalisar da aka yi a farkon mako, zaben da bai samu gudana ba a yankin Tigray saboda rikici.

A cikin watan Nuwamban shekarar 2020 Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya baiwa dakarunsa umarnin afkawa ‘yan tawayen yankin Tigray da zummar kawar da gwamnatin da ya bayyana a matsayin barazana ga tsaron kasar.

Sai dai bayan shafe kusan watanni 8 da ana gwabza yaki a yankin na Tigray dubban mutane sun tagayyara bayaga rasa muhallansu, inda a baya bayan nan Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutane akalla dubu 350 na gaf da fadawa cikin bala’in yunwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.