Isa ga babban shafi
Habasha-Sudan

Sojojin sa kai na Tigray na neman mafaka a Sudan bayan kare aiki a Darfur

Sojojin samar da zaman lafiya daga Yankin Tigray na kasar Habasha da suka yi aiki a Darfur sun nemi mafakar siyasa a Sudan saboda abinda suka kira fargabar azabtar da su idan suka koma gida.

Tun cikin watan Nuwamban bara rikici ya barke a yankin Tigray na Habasha
Tun cikin watan Nuwamban bara rikici ya barke a yankin Tigray na Habasha REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

An dai shirya kwashe wadannan dakaru ne da ke aiki a karkashin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka ta AU daga Darfur a ranar 31 ga watan Disamba domin mayar da su gida bayan kawo karshen aikin su, amma Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan 120 daga cikin su sun ce ba za su koma gida ba.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya yi magana da wasu daga cikin su da suka samu mafaka a sansanin Um Gargour kuma sun tabbatar da gabatar da bukatar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.